08 RABE-RABEN
TRADERS A KASUWA
Trading
• Trading (cinikayya) na nufin saye da siyarwar kadara ko haja (assets).
• Misali, idan ka sayi kayan abinci a kasuwa ko kuma a shago, wannan ana kiranshi
cinikayya.
• Idan ka canja tsohuwar wayarka aka baka sabuwa, shima wannan ana kiranshi
cinikayya.
• Idan ka saida Naira ka karbi Crypto, shima ana kiransa cinikayya.
1
Rabe-Raben traders a kasuwar crypto
• Scalping (Cinikayyar sauri)
• Day Trading (Cninikayyar yini guda)
• Swing Trading (Cininikayyar matsakaicin zango)
• Positional Trading (Zuba jari)
2
Scalping – Cinikayyar gajeren lokaci
• Scalpers suna amfani da karamar juyawar farashi cikin sauri, sau da yawa suna shiga
kasuwa su kuma fita acikin mintuna (ko kuma sakanni).
• Scalping na professional traders ne da suke da ilimi mai zurfi akan Technical analysis
a kokarinsu na hasashen juyin da kasuwa zata yi.
• Saboda karancin lokaci, scalpers suna bin karamar riba kamar 1% .
3
Day Trading – Cinikayyar yini guda
• Daytrading: Cinikayyar yini guda, ita ce zaka gani da yawa a fina-finai da suka
kunshi masu kasuwar hannun jari na Wall Street.
• Day traders suna zama kamar rabin yini zuwa kwana biyu a kasuwa.
• Day trading yana bukatar kwarewa a technical analysis, kuma suna bin riba kamar
5-10% .
4
Swing Trading – Cinikayyar matsakaicin zango
• Kowane coin yana da nashi cycle, wanda yawanci yana kai sati guda zuwa wata guda.
• Swing Trader yana rike coin na tsawon sati guda zuwa wata guda don dacewa da
wannan cycle.
• Swing trading yana bukatar dan karamin ilimin technical analysis, kuma swing traders
suna bin riba kamar 50-100% .
• Alkaluma na trading sun nuna cewa, swing traders su ne suka fi samun nasara a
cryptocurrency trading
5
Investing/Long term Trading – Cinikayyar dogon zango ko
Zuba jari
• Investment na nufin rike coin na dogon zangon lokaci kamar wata shida zuwa shekaru
biyar (5).
• Investors suna amfani da ilimin Fundamental analysis wajen binciko tokens masu
inganci musamman sabbin narratives.
• Investing a coin na tsawon lokaci yana bada riba sosai idan aka dace, dole investor
ya rika bibiyar token da yake rike dasu lokaci zuwa lokaci.
• Investor yana maida hankali ne akan Marketcap wajen kirga riba, sabanin price.
6
Bitar Aji
• Traders sun kasu gida-gida a kasuwar cryptocurrency. Akwai scalpers, day
traders, swing traders sai investors. Kowane kashi na trader da abinda yake
nema a kasuwa na riba, da kuma dadewar da yake yi a kasuwan.
• Kwarewa da kuma zangon lokaci su suke banbanta traders.
7
Aikin Aji
Kawo rabe-raben traders da muke da su a kasuwa.
Yi bayani akan Swing trading tare da kawo dalilai da kake gani suka sanya shi
yafi zama mafi samun nasara akan sauran rabe-raben traders.
Wane nau’in trader kake sha’awar zama a kasuwa nan gaba?
Shin aikinka ko sana’arka zai baka isashshen lokaci a gaban computer don
zama scalper ko day trader?